DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a yi wa matasan NYSC karin kashi 100 na alawus a jihar Zamfara

-

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na ya ba da umarnin kara yawan alawus-alawus na matasa masu yi wa kasa hidima, NYSC, da za su yi aiki a jihar da kashi 100 cikin 100.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Gusau, yayin da yake bude sansanin masu yi wa kasa hidima Batch ‘A’ na 2025 a jihar.

Google search engine

Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Abubakar Nakwada a wajen taron, ya nanata kudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da jin dadin daukacin mambobin su 550 da aka tura jihar.

A wajen taro ya sanar da cewa an bayar da umarnin a dawo da biyan alawus-alawus tare da karin wani kaso ga duk masu yi wa kasa hidima da ke jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An dage jana’izar marigayi Muhammad Buhari zuwa ranar Talata -Dikko Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da shirye-shiryen jana'izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli,...

Jam’iyyar ADC ta sanar da kwana uku na alhinin rashin tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari

Jam’iyyar ADC ta bayyana kwanaki uku na zaman makoki ga mambobinta don girmama marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi...

Mafi Shahara