DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu a Kano ta daure wani mutum saboda laifin sare bishiya ba bisa ka’ida ba

-

Wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki dake jihar Kano, ta yanke wa Inuwa Ayuba hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari tare da zabin biyan tara bisa samunsa da laifin sare bishiryar darbejiya bakwai ba bisa ka’ida ba a kauyen Sarauniya, karamar hukumar Dawakin Tofa.

A cewar lauyan mai shigar da kara, Bahijja H. Aliyu, wata tawagar masu sa ido daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, ta yi gaggawar dauki matakin bisa wannan abu da mutumin ya yi, kuma sai da ta tattara shaidu kafin gabatar da shi a gaban kotu.

Google search engine

Matakin ya sabawa dokar muhalli da dazuzzuka da kuma gurbatar muhalli ta jihar Kano, wadanda suka haramta sare bishiya ba tare da izini ba.

Bayan duba shaidun, kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi, inda ta yanke masa hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari ko kuma biyan tara. Bugu da kari, an umarce shi da ya dasa bishiyar darbejiya guda 14 a matsayin wani bangare na hukuncinsa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan sanda sun koka da yawan yada labaran karya a Nijeriya – IGP

Shugaban 'yan sanda a Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya ce babu wata hukuma a Najeriya da ke fuskantar mummunan tasiri daga labaran karya kamar ‘yan...

Amurka ta fara gamsuwa da matakan Tinubu kan tsaron Nijeriya

Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto yara 100 da aka sace daga St. Mary’s Private Catholic School a...

Mafi Shahara