DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dole mu sake ba Tinubu dama a 2027 ya karasa aikin da ya dauko – Minista Festus Keyamo

-

 

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bukaci ‘yan jam’iyyar APC da su manta da bambancin ra’ayi da son zuciya, su marawa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake samun nasara a zaben shekarar 2027.

Google search engine

 

                                   Festus Keyamo

Keyamo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels Television a ranar Litinin, inda ya jaddada cewa dole ne a sake zaɓen Tinubu domin ya kammala sauye-sauyen da ya fara a harkokin mulki da tattalin arziki.

A cewar Ministan, nasarar cigaba da aiwatar da sauye-sauyen na bukatar hadin kai da fahimtar juna daga cikin jam’iyyar, tare da dagewa wajen tabbatar da dorewar ayyukan da aka rigaya aka fara.

Festus Keyamo, ya bayyana dalilin da ya sa ya mika shugabancin tsarin jam’iyyar APC ga Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, wanda kwanan nan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar mai Mulki, inda yace ya zama wajibi a hada kai da karfafa gwiwar sabbin ‘yan jam’iyyar da suka dawo domin ci gaban jam’iyyar a matakin jiha da kasa baki daya kafin tafiyar ta kai gacci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai zama a San Gabriel Valley, Abiola Femi Quadri, hukuncin ɗaurin shekara 11 da wata...

Natasha ta sake shan alwashin komawa majalisar dattawa a ranar Talata

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar Majalisar Dattawa daga jihar Kogi da aka dakatar, ta shigar da ƙara ga Majalisar Dattawa tana neman su girmama hukuncin Babbar...

Mafi Shahara