Masana ALQUR’ANI daga kasashe 20 ne zasu shiga gasar karatun ALQUR’ANI ta duniya kuma ta farko a Najeriya wanda tsohon Dan Majalissar Wakilai Mai wakiltar mazabar Bassa da Jos ta Arewa a Jihar Plateau Honourable Muhammad Adam Alkali OON ya dauki nauyin shiryawa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Muhammad Bashir, jami’in hulda da jama’a na cigiyar shirya gasar karatun Alqur’ani ta kasa da kula da marayu wato National Council For Orphan Quranic Recitation Competition.
Gasar wadda zata gudanaa a watan Ogustan wannan shekarar, za a fara ta ne a Birnin Jos Jihar Plateau sannan a kammala a Babban Birnin Tarayya Abuja.
A lokacin gagarumin taron kaddamar da kwamitocin shirye shiryen gudanar da gasar ta duniya, Wanda Gwanayen Qur’ani daga fadin kasar nan Suka halarta, Honourable Alkali yace tuni an sanar da
cibiyar bunkasa karatun addinin musulumchi ta Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta Sokoto ta goyi bayan kudirin.
Yace gasar nada nufin habbaka harkokin addinin musulunchi da hadin kan Musulmi, yana Mai bayyana mahimmancin karanta ALQUR’ANI Mai Girma Wanda shine Babban malamin dake wanke zuciya da samar da shiriya ga al’ummar Musulmi.
Da yake alkawarin cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, honourable Alkali ya bada misalin yadda wani bawan Allah yayi kokarin shirya gasar karatun ALQUR’ANI ta duniya amma ba a samu nasara ba saboda wasu kalubale da aka fuskanta.
A jawabin sa, Shugaban kwamitin shirye shirye Gwani Sadiq Zamfaraya yi bayanin irin ayyukan da kwamitin ya gudanar da nufin ganin an samu nasarar gudanar da gasar ba tare da matsala ba, sannan ya yi godiya ga wanda ya dauki nauyin shirya gasar.
Kasashen da ake tsammanin zasu halarchi gasar sun hada da Kamaru da Ghana da Chadi da Senegal da Kenya da Tanzania da Mauritania da Masar da Morokko da Libya da Algeria da Saudiya da Kuwait da Qatar da Malaysia da Ingila da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa da Amurka.
Ko wace Kasa zata zo da mahalarta gasar maza da mata da kuma hukumomin su.