Gwamnatin Nijeriya ta ce ta fara aiwatar da tsarin karatu a dukkan kwalejojin ilimi na tarayya, wanda zai bai wa kwalejojin damar ba da takardar shedar malanta a Nijeriya da kuma Digiri na farko a fannin ilimi.
Wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo ya fitar, ya ce wannan ya biyo bayan dokar kwalejojin ilimin tarayya ta 2023 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu.
Da yake kaddamar da tsarin a Abuja, Ministan Ilimi Dokta Tunji Alausa ya nuni da cewa wannan gagarumin ci gaba ne da zai sake fasalin ilimin a Nijeriya.