DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Naira ta kara faduwa a kasuwar canji ta Gwamnati — CBN

-

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar canji ta hukuma, inda ta rufe a kan N1,602.18 kan kowacce dala a ranar Juma’a, 2 ga Mayu, 2025. Wannan na nufin a samu faduwar Naira da N5.49 ko kuma kashi 0.34 cikin 100 idan aka kwatanta da farashin da ta tsaya a kai a ranar Laraba, 30 ga Afrilu, na N1,596.69.

Masana sun danganta wannan faduwar da hauhawar bukatar kudin waje da kuma karancin isar sa daga hannun gwamnati da masu zuba jari. A cewar bayanan kasuwar canji, farashin canjin Naira ya tsaya tsakanin N1,599.95 da N1,596.69 daga ranar Litinin zuwa Laraba kan dalar Amurka daya.

Google search engine

A kasuwar bayan fage (black market), Naira ta dan samu karuwa, inda ta tashi daga N1,608 zuwa N1,605 kan kowacce dala a ranar Juma’a.

Wannan ci gaba na nuna cewa, duk da kokarin da CBN ke yi na daidaita kasuwar canji, har yanzu ana fuskantar kalubale wajen daidaita darajar Naira a kasuwannin canji na cikin gida da na waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Lakurawa sun yi ajalin makiyaya goma a jihar Kebbi

Aƙalla makiyaya goma ne aka ruwaito sun rasu a harin ramuwar gayya da aka kai wa Fulanin kauyen Tilli da ke Ƙaramar Hukumar Bunza ta...

PDP ta dage tantance ‘yan takara na babban taronta na kasa

Dagewar ta zo ne ’yan sa’o’i bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ayyana shirinsa na takarar shugabancin jam’iyyar, duk da cewa wasu...

Mafi Shahara