DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnonin PDP sun cimma matsaya da Wike don ceto jam’iyyar kafin zaben 2027

-

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa akwai sabuwar yarjejeniya tsakanin wasu gwamnonin jam’iyyar PDP da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da nufin kawo zaman lafiya da hadin kai cikin jam’iyyar kafin babban zaben shugaban kasa na 2027.

Wani babban jigo daga cikin jam’iyyar ya shaida wa Sunday Punch cewa Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ne ya wakilci gwamnonin PDP a wani muhimmin zama da suka yi da Wike a birnin Legas makon jiya.

Google search engine

Majiyar ta bayyana cewa taron ya maida hankali ne kan rikicin siyasa da ke faruwa a jihar Ribas tsakanin Wike da gwamnan da aka dakatar Siminalayi Fubara. Haka kuma sun tattauna batutuwan shugabancin yankin Kudu maso Kudu na jam’iyyar da kuma mukamin Sakataren jam’iyya na kasa da har yanzu ba a warware ba tun Disambar 2024.

Jam’iyyar PDP dai tana fama da rikice-rikice na cikin gida tun bayan kammala zaben 2023, kuma yunkurin sulhu da kwamitocin jam’iyyar – ciki har da NWC, BOT, NEC da kuma Gwamnonin PDP – suka yi, ya ci tura, maimakon magance matsalolin sai kara rura wutar rikici.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Buhari mutum ne mai girmama al’adu da masarautu – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shiga sahun wadanda ke jimamin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a...

An rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat Buhari

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin girmamawa da...

Mafi Shahara