Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce Nijeriya a yanzu ta zama kasar da ta fi kowacce yawan yara masu fama da tamowa a Afirka.
Hukumar ta kasa da kasa ta bayyana hakan a shafinta na yanar gizo ranar Talata, inda ta kara da cewa a halin yanzu duk yara biyu cikin 10 na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Ya ce kimanin yara miliyan biyu a Nijeriya da ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, kuma ita ce ta biyu a yawan yara kanana a duniya masu tamowa a duniya.