DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Abba a Kano ta haramta gabatar da shirin siyasa kai tsaye a kafafen yada labarai

-

Gwamnatin jihar Kano ta haramta gabatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a gidajen rediyo da talabijin, jihar. Hakan na a matsayin wani matakin da ta ce ta dauka don kare tarbiyya da kuma dakile yaduwar kalaman da ka iya tunzura jama’a.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da shugabannin kafafen yada labarai, inda ya jaddada bukatar bin ka’idojin aikin jarida da ke girmama dabi’u da addinin al’ummar jihar.

Google search engine

A cewar Waiya, wannan haramcin ba wata hanya bace ta danne ra’ayoyin siyasa, illa dai dabarar hana yada kalaman tunzuri ko batanci da za su iya tayar da hankali ko kuma dagula tarbiyyar al’umma.

Daya daga cikin muhimman matsayar da aka cimma a taron shi ne cewa duk wani da zai je kafafen yada labarai sai ya sa hannu kan takardar yarjejeniyar kauce wa furuci cin mutunci, kage ko saba wa al’adun jama’a. Haka kuma an gargadi masu gabatar da shirye-shirye da su guji tambayoyin da ka iya janyo martani mai zafi ko na batanci ko tunzuri a cikin shiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sabon shugaban hukumar zaben ya yi alwashin dawo da ingantacce da sahihin zabe a Nijeriya

Sabon shugaban hukumar zaɓen Nijeriya, INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya sha alwashin dawo da sahihanci da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe na ƙasar, yana...

Ba ni ke tsoma baki a gwamnatin Kano ko raba kwangiloli ba – Rabi’u Musa Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya karyata zargin da ake yi masa na tsoma baki a harkokin mulkin...

Mafi Shahara