DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babu karar-kwana, da tuni na bakuncin lahira a zanga-zangar #EndSARS – Jarumi a Nollywoood Desmond Elliot

-

Fitaccen ɗan wasan fina-finan Nollywood kuma ɗan siyasa, Hon. Desmond Elliot, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga wani hari da wasu baƙin fuska suka yi ƙoƙarin kai masa a lokacin zanga-zangar #EndSARS da ta girgiza Najeriya a shekarar 2020.

Elliot, wanda ke wakiltar mazaɓar Surulere a Majalisar Dokokin Jihar Legas karkashin jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a yayin da yake tuna mawuyacin lokacin da matasa suka gudanar da zanga-zanga domin neman a rusa rundunar SARS ta ’yan sanda.

Google search engine

Sai dai duk da haka, Elliot ya tsallake rijiya da baya daga harin da aka shirya kai masa, inda ya nuna godiya ga Allah bisa cetonsa daga hadarin da ka iya zama ajalinsa.

Elliot, wanda ya fada siyasa a shekarar 2015, ya fuskanci zazzafar suka a wancan lokaci bayan bullar wani bidiyo da ya nuna shi yana kiran matasan Najeriya da “yara” a wani zaman majalisar dokokin Jihar Legas furicin da ake ganin ya ƙara tunzura jama’a matasan su kai masa farmaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wasu ‘yan Jam’iyyar APC sun nemi Tinubu da ya sauke ministan Abuja Nyesom Wike daga mukaminsa

Wasu shugabanni a jam’iyyar APC, ƙarƙashin APC Leaders Forum da Tinubu/Shettima Solidarity Movement, sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta cire Nyesom Wike daga muƙamin...

Gwamnatin Nijeriya za ta bai wa ‘yan wasan Super Eagles alawus-alawus na AFCON

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa an kammala dukkan matakai tsaruka domin biyan alawus-alawus na wasannin Super Eagles a gasar AFCON 2025, inda ta ce 'yan...

Mafi Shahara