Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya mayar da Naira miliyan 301 zuwa baitul malin jihar, daga cikin Naira biliyan 4 da miliyan dari 800 na kasafin kudin shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan.
A yayin wata gajeriyar liyafa a Dutse babban birnin jihar, kwamishinan ya bayyana cewa bayan aiwatar da shirin ciyar da jama’a yadda ya kamata, an samu ragowar kuɗi, kuma saboda gaskiya da amana, ya mayar da su domin al’umma.
Kungiyoyin fararen hula da al’umma sun bayyana jin daɗin su da wannan ɗabi’a ta gaskiya daga Kwamishina Sankara, tare da kiran sauran jami’an gwamnati da su yi koyi da irin wannan tsari na adalci da gaskiya.