DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

-

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su a ofishin ‘yan sanda na tsawon lokaci.

Sakin nasu ya zo ne bayan gabatar da su gaban alkali a kotun jihar Agadez a yau Juma’a, inda aka saurari batunsu bisa zargin da ake musu da kuma irin aikinsu na jarida.

Google search engine

Wannan na zuwa ne kasa da makonni biyu da aka gudanar da bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta shekarar 2025, kan yadda hukumomin tsaro ke mu’amalantar ‘yan jarida a sassan duniya, musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikice.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai zama a San Gabriel Valley, Abiola Femi Quadri, hukuncin ɗaurin shekara 11 da wata...

Natasha ta sake shan alwashin komawa majalisar dattawa a ranar Talata

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar Majalisar Dattawa daga jihar Kogi da aka dakatar, ta shigar da ƙara ga Majalisar Dattawa tana neman su girmama hukuncin Babbar...

Mafi Shahara