DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jami’an tsaro sun ceto ‘yan kasar Ivory Coast 25 tare da cafke masu garkuwa da mutane

-

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama wasu mutane takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wani aikin samame da ta yi nasarar kubutar da ‘yan kasar Ivory Coast 25 daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Mai magana da yawun ‘yan sandan na kasa ACP Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa, aikin da hukumar ta yi ya kai ga cafke mutanen ya fara ne a lokacin da wata ‘yar kasar Ivory Coast mai suna Kaussi Amenan Marianman ta gabatar da rahoto a bban ofishin hukumar tsaro NCB da ke Abidjan a ranar 23 ga Afrilu, 2025, cewa wasu mutane biyu, Simon da Oliver da Michael Odunga ne su yaudare danta, ya yi balaguro zuwa Nijeriya domin samun takardun zuwa kasar Belgium.

Google search engine

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya kudin fansa CFA milyan 2.5, kwatakwacin milyan 6.6 a lokacin da aka kama shi a Nijeriya.

Bayan samun cikakken bayanan sirri akan batun ga hukumar NCB Abidjan. kwamishinan ‘yan sandan kasa da kasa INTERPOL a Legas, Bode Ojajuni, ya aika da tawagar masu bincike domin ceto wanda ake tsare dashi tare da kamo wadanda suka yi garkuwa da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara