Gwamnonin jam’iyyar PDP za su yi taro a Abuja akan sauyin shekar da ‘yan jam’iyyar ke yi a kwanakinnan.
Wannan ya biyo bayan ficewar gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori da Dr. Ifeanyi Okowa, da sauran ‘yan jam’iyyar PDP a jihar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Gwamnonin sun gana makonni uku da suka gabata a Ibadan inda suka bayyana cewa jam’iyyar ba za su shiga tattaunawar hadaka da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ke jagoranta ba.
Gwamnonin za su yi taron ne a gidan gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad da ke Asokoro a Abuja da nufin shawo kan matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar.