Wani na hannun damar rikakken dan bindigar nan Bello Turji, mai suna Danbokolo ya kai hari a wasu kauyukan jihar Sokoto.
Daga cikin kauyukan ha da mahaifar tsohon gwamnan jihar Attahiru Dalhatu wato Bafarawa.
Kauyukan su ne Gebe, Kamarawa, Garin Fadama, Bafarawa da Haruwai.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Danbakolo ya kai harin ne a matsayin ramuwar gayya kan farmakin da sojoji suka kai wa ‘yan ta’addar.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar Asabar.