DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ni ne na sa PDP ta shahara a Nijeriya – Wike

-

Ministan babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja Nyesom Wike, ya bayyana cewa yana daga cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da shaharar jam’iyyar PDP tare da kafa ta a matsayin babbar jam’iyya mai tasiri a matakin kasa da jihohi.

Wike ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta kai tsaye da ya yi da manema labarai a Abuja.

Google search engine

Yayin da yake martani ga suka da wani jigo a jam’iyyar PDP kuma mamba na kwamitin amintattu na jam’iyyar, Chief Bode George, ya yi dangane da rufe hedikwatar jam’iyyar ta kasa, Wike ya shawarci dattijon siyasar da ya zauna a gidansa ya ci gaba da karanta jaridu idan babu abin da yake yi.

Ya kara da bayyana cewa ba shi ko jam’iyyar za su iya biyan kudin haraji (ground rent) ba, domin kadarar ba a rubuta ta da sunan su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

NAHCON ta gargadi maniyyata Hajjin 2026 na Nijeriya kan yin rijista da wuri

By Fatima Aminu Dabo Hukumar jin daɗin alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da jadawalin aikin Hajjin 2026, inda ta bayyana cewa 20 ga Maris, 2026...

Ana ci gaba da neman wata dattijuwa bayan kifewar kwale-kwale dauke da fasinja 11 a Sokoto

An gano gawar wani matashi mai shekara 29 da ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Jihar Sokoto.Lamarin ya faru...

Mafi Shahara