Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi kira da a sauya tsarin mulki domin bai wa masu mukaman siyasa da aka zaba a matakai daban-daban na gwamnati damar yin wa’adi guda na shekaru biyar ko shida kacal, maimakon wa’adin biyu na shekaru hudu-hudu da ake yi a yanzu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da wasu Musulmai da suka hada da malamai, sarakunan gargajiya da masu rike da mukaman siyasa suka kai masa ziyara a gidansa da ke Ikolaba, Ibadan, bayan kammala sallar layya da aka gudanar a filin idi na Agodi, Ibadan.



