Gwamnatin jihar Kano ta nemi gwamnatin tarayya ta biya diyya sakamakon soke bukukuwan hawan sallah da aka yi a jere tsawon shekaru biyu.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Tajo Uthman, ne ya bayyana hakan a lokacin da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya kai gaisuwar Sallah ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar.
Uthman ya ce jihar ta yi asarar kudade masu yawa saboda dakatar da wannan biki na al’ada da ake gudanarwa a kowace shekara, wanda ke jan hankalin masu yawon bude ido na cikin gida da na kasashen waje.