Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya Bello Matawalle, ya marabci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zuwa jam’iyyar APC.
Ministan ya bayyana hakan ne a gidansa da ke garin Maradun, yayin da yake karɓar dubban magoya bayansa da suka zo masa gaisuwar sallah.
Matawalle, ya ce jam’iyyarsu ta APC jam’iyya ce ta shugabanni masu kima da biyayya, inda ya bukaci Dauda Lawal da ya bar shakku ya shiga jam’iyyar masu kishin ci gaban kasa domin ci gaban jihar Zamfara.
Matawalle ya jaddada cewa maimakon Gwamna Lawal ya rika fakewa da boye-boyen shiga jam’iyyar, ya kamata ya fito fili ya bi hanyar da ta dace don shiga APC, maimakon irin wasan ɓuya da yake yi yanzu.
Ya ce bai da wata ƙyama ko ƙin amincewa da Gwamnan ya shiga jam’iyyar, don haka ya shawarce shi da ya rungumi jam’iyyar domin ya kasance cikin jerin jagororin da ke fafutukar tabbatar da tsaro, ci gaba, zaman lafiya da walwala a kasar nan.
Ministan ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sa na jagoran ‘yan cigaba, ƙwararren mai tafiyar da al’amuran zaman lafiya ne, kuma kullum yana mai da hankali kan ci gaban kasa. Ya ce Shugaba Tinubu na maraba da kowa da kowa da ke da niyyar shiga sahun masu kishin ci gaban Nijeriya.
Dr. Bello Matawalle ya tabbatar wa da dimbin magoya bayansa cewa yana da cikakken ƙuduri wajen kula da jin dadinsu da rayuwarsu, inda ya bukace su da su ci gaba da mara wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin aiwatar da ajandar “Renewed Hope”, musamman a fannonin tsaro, noma, kiwon lafiya, walwala da ci gaban tattalin arziki.
Ya kara da cewa Shugaban Kasa na da ƙaunar Jihar Zamfara a zuciyarsa, kuma kullum yana sa ido wajen ceto jihar daga halin rashin tsaro da matsin tattalin arziki da take ciki. Ya bukaci jama’ar jihar da su bai wa gwamnatin Tarayya cikakken goyon baya da hadin kai domin ganin wannan buri na Shugaban Kasa ya tabbata.
Ministan ya tunatar da irin matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka na kawar da manyan shugabannin ‘yan ta’adda da mabiyansu, wadanda suka addabi jihar da yankin Arewa gaba ɗaya. Ya ce Shugaban Kasa kwanan nan ya bai wa hukumomin tsaro umarnin kawo karshen matsalar tsaro a Arewa kafin ƙarshen shekarar nan, kuma ma’aikatar tsaro da manyan hafsoshin tsaro na aiki tukuru domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni.
Sai dai ya zargi gwamnatin jihar Zamfara da rashin yin abin a zo a gani wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar, inda ya ce maimakon haka gwamnatin ta shiga cikin yaudarar jama’a.
Ya ce a zamaninsa a matsayin gwamna, mutane sun shaida kuma sun amfana da matakan tsaro, ‘yanci, jin dadi da walwala, sabanin abin da ke faruwa a yanzu a karkashin Gwamna Lawal, inda har ‘yan jam’iyyar PDP ke kuka da salon mulkin jihar.
Tsohon gwamnan ya nuna damuwa da karancin kudin shiga da yake samu a lokacin gwamnatinsa, inda ake samun tsakanin biliyan 3 zuwa 4 a kowane wata, sabanin yanzu da Gwamna Lawal ke karɓar tsakanin biliyan 19 zuwa 24 a kowane wata daga asusun tarayya. Don haka ya kalubalanci Gwamna Dauda Lawal da ya bayyana adadin kudin da yake samu a kowane wata, domin a tantance ko sun dace da ayyukan ci gaban da yake ikirarin ya aiwatar a jihar.