Ofishin mataimakin shugaban kasa ya mayar da martani ga kalaman Sanata Datti Baba-Ahmed, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, wanda ya yi suka kan matakin da shugaba Tinubu ya dauka na ci gaba da barin mataimakinsa Kashim Shettima akan karagarsa.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Mataimakin Shugaban kasar, Stanley Nkwocha, ofishin ya bayyana kalaman na Baba-Ahmed a matsayin” kalamai marasa kan gado” wadanda shugaban kasa da mataimakinsa basu da lokacin sauraronsu, kasancewar sun mayar da hankali kan ayyukansu na gina Ć™asa.
Sanarwar ta kuma bayyana irin nasarorin da mataimakin shugaban kasa Shettima ya samu da ma kwarewarsa akan aiki da ta haɗa da gogewarsa a harkar koyarwa da bayar da ilimi da kasancewarsa ma’aikacin banki, sannan kwamishina, sannan gwamna gwamna, kana sanata, kafin ya zama Mataimakin ShugabanKasa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Shettima na biyayya ga shugaba Tinubu kamar yadda yake nuna jajircewarsa kan tabbatar da ajandar sabunta fata ta Renewed Hope a turance.
Ofishin ya kuma tunatar da Baba-Ahmed abubuwan da suka faru a baya, da suka hada da cire shi daga majalisar dattawa a shekarar 2011 bayan da aka zarge shi da magudin zabe inda ta ƙara da cewa, zantukan na Baba Ahmed watakila ba za su rasa nasaba da ƙwaɗayinsa na ɗarewa kowace irin kujerar mulki ba ko da kuwa ta haramtacciyar hanya ce, musamman ma kujerar Mataimakin Shugaban kasar wadda Datti Baba-Ahmed din ya sha kaye a takararta a zaɓen bara sakamakon karawarsa da gogaggen ɗan siyasa ɗan asalin Arewa wanda ke da tarin abin faɗa na nasarori a ajandar sabunta fata ta Shugaban Kasa.