Tsohon Ministan Matasa da Cigaban Wasanni a Nijeriya, Solomon Dalung, ya bayyana cewa duk da wasu muhimman nade-nade ko dabarun siyasa, Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC za su sha kaye a babban zaben shekarar 2027.
Da yake magana a tashar talabijin ta News Central, Dalung ya yi watsi da tasirin sauya sheka ko nade-naden da Shugaba Tinubu ke yi, yana mai cewa ra’ayin jama’a ne zai yi rinjaye.
Ya kara da cewa ko da gwamnoni 36 suka koma APC, kuma ya nada Seyi Tinubu a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, har ma ya nada matarsa a matsayin Babbar Alkalin Alkalan Nijeriya, kuma ko da INEC ce ta zama cibiyar karshe da ta sauya sheka zuwa APC, za su sha kaye a 2027.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da kaddamar da yaki a kan al’ummar Nijeriya, yana mai nuna halin kuncin rayuwa da kuma abin da ya kira rashin adalci da gwamnati ke daukar nauyinsa.
I’m