Matatar Dangote ta bayyana cewa ta gano wata sabuwar makarkashiya da wasu yan kasuwa ke yi, inda suke karkatar da man fetur da aka sayar musu a rangwame zuwa hannun wasu dillalai da ba su da rajista — domin cin haramtacciyar riba.
Sakamakon haka, kamfanin ya dakatar da tsarin sayar da mai da rangwame da ya kirkiro da shi domin tallafawa dillalai da ‘yan kasuwa.
Matatar ta bayyana haka ne a cikin wata takarda da ta aike wa dukkan abokan hulɗar kamfanin a ranar 13 ga Yuli, 2025, wacce Fatima Dangote, daraktar huldar kasuwanci ta kamfanin, ta sanya wa hannu.
Takardar ta bayyana cewa an dakatar da tsarin har sai an kammala bincike tare da sake tsari na tabbatar da gaskiya da adalci.

Dangote ya dakatar da tsarin sayar da mai da rahusa bayan gano wasu ‘yan kasuwa suna karkatar da man
-