DCL Hausa Radio
Kaitsaye

DCL Hausa ta yaye daliban Aikin Jarida na Zamani (Kashi na Farko, 2025)

-

DCL Hausa na alfahari da kokarin da take na bayar da gudummawa wajen gina matasan ‘yan jarida ta hanyar shirin “Koyon Sanin Makamar Aiki” wato internship ga ɗalibai matasa masu sha’awar aikin jarida.

Wannan shafi na musamman yana nuna daliban da suka kasance tare da mu a zangon farko na shirin daga 01.05.2025 zuwa 31.07.2025. 

Google search engine

1. Muhammad Jamil Ibrahim

“Tabbas, zama na a DCL Hausa a matsayin intern ya ba ni damar koyon abubuwan da dama game da aikin jarida musamman a zamanance. Tun daga hada script, zakulo labarai masu daukar hankali, hada rahoto da kuma tace sauti da hoto mai motsi da kuma yadda zan fuskanci na’urar daukar hoto.”

Shawararsa:
“Ina shawartar wadanda suka samu damar koyon aiki da DCL Hausa da su kasance masu amfani da wannan damar wajen mayar da himma da kuma maida hankali wajen fahimtar yadda tsarin aikin jarida yake a zamanance.”

Wasu daga cikin ayyukan da yayi:

2. Salim Muhammad Gali

“A yayin wannan horon na samu cikakkiyar fahimta da ƙwarewa a fannonin da dama na aikin jarida na zamani musamman wajen shirya explainer videos, inda na koyi yadda ake tsarawa da gabatar da bayanai cikin salo mai sauƙi da ilmantarwa ga masu kallo, karanta labarai da kuma babbance sahihan labarai da na bogi.”

Shawararsa:
“Ka kasance mai mutunta lokaci, ka koyi karɓar gyara, kuma kada ka ji nauyin tambaya. DCL Hausa na da yanayi mai cike da ƙwarewa da fasaha – ka yi amfani da wannan damar don gina iyawarka a cikin kwararrun yan jarida.”

Wasu daga cikin ayyukan da yayi:

3. Salisu Ado Sulaiman

“Daga cikin abubuwan da na amfana da zama na a DCL Hausa akwai samun gogewa ta fannoni da dama da suka haɗar da tsara rubutu ta yadda zai ja hankali matuƙa, karantawa ko gabatar da shi cikin salo, da kuma gabatar da bidiyo explainers da rahotanni.”

Shawararsa:
“Na samu cikakkiyar dama ta yin cudanya da gogaggun ‘yan jarida da suka dade a fannin – wannan ilimi ne babba wanda ya gina min kwarin gwiwa.”

Wasu daga cikin ayyukan da yayi:

Sakon Kodineta:

Tabbas, wadanan ɗalibai matasa masu sha’awar aikin jarida kashi na farko a 2025, sun nuna irin hazaka, ƙwarewa, da himma ta matasa ƴan jarida a lokacin da suke Koyon Sanin Makamar Aikia DCL Hausa. Muna fatan wannan ƙwarewar za ta zama ginshikin nasarar su a gaba.

Ukashatu Ibrahim Wakili

Mai Kula da Shirin Sanin Makamar Aiki na DCL Hausa (Internship Coordinator)

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Daga 2026 ₦500,000 kawai ɗan Nijeriya zai iya cira a banki cikin sati ɗaya – CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake fasalin dokokin cire kuɗi daga bankuna kan sabon tsarin da zai fara aiki daga watan Janairun 2026. Babban bankin ya...

Ƴan kwangila sun girke akwatin gawa a ofishin ma’aikatar kuɗin Nijeriya

‘Yan kwangila sun girke akwatin gawa a kofar shiga ofishin ma’aikatar kudin Nijeriya da ke Abuja.   ‘Yan kwangilar, karkashin inuwar kungiyarsu ta 'yan asalin Nijeriya sun...

Mafi Shahara