Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire na Najeriya Geoffrey Nnaji ya yi murabus daga mukaminsa biyo bayan cece-kuce kan zargin sa da yin amfani da takardun karatu na bogi.
Labari mai alaka: Sakataren gwamnatin Jihar Bauchi ya yi murabus daga mukaminsa
Nnaji, wanda aka nada a watan Agustan shekarar 2023, ya sanar da murabus din nasa ne a cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban a ranar Talata, inda ya yi godiya bisa damar da aka ba shi ta yi wa kasa hidima.
Gabanin daukar wannan mataki, Nnaji ya ce akwai abokan hamayya a siyasa da ke ta yunkurin bata masa suna.
Labari mai alaka: An sallami daraktoci 33 daga aiki a ma’aikatar sufurin sama
Murabus din nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan sahihancin takardun karatunsa daga Jami’ar Nsukka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



