DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jiragen sojin Amurka sun fara sauka a Maiduguri

-

Jiragen sojin Amurka sun fara sauka a birnin Maiduguri, Jihar Borno, a wani sabon mataki na haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya.

Kamar yadda jami’ai suka bayyana, wani jirgin sojin Amurka ya sauka a daren Alhamis a filin jirgin saman Maiduguri, yayin da ake sa ran ƙarin jirage za su iso a ƙarshen mako.

Google search engine

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kusan jami’an Amurka 200 ne, ciki har da masu nazarin bayanan sirri, masu ba da shawara da masu horaswa za su zo Nijeriya.

alibin jiragen nau’in C-17 ne masu ɗaukar kaya, waɗanda ke kawo jami’ai da kayan aiki domin tallafa wa rundunonin tsaron Nijeriya a yaƙi da matsalolin tsaro a arewa maso gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wike ya ja layi da wanda ba sa goyon bayan Tinubu

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce zai mara wa duk dan takarar da ke goyon bayan Shugaban Kasa, Bola Tinubu, baya a...

Tinubu zai kai ziyara jihar Adamawa a ranar Litinin

Shugaban kasa, Bola Tinubu, zai kai ziyara ta aiki jihar Adamawa ranar Litinin, kasa da sa’o’i 48 bayan irin wannan ziyara da ya kai a...

Mafi Shahara