DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Fada ya kaure tsakanin wasu direbobi da manajojin Dangote a Obajana

-

Wasu bayanai da DCL Hausa ta samu na cewa wani hargitsi ya kaure tsakanin wasu direbobin motocin kamfanin Dangote da ke kamfanin na Obajana a jihar Kogi da wasu manajojin kamfanin.
Majiyar DCL Hausa da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce rikicin har ya yi sanadiyyar ji wa wasu daga cikin manajojin raunuka munana.
“Da idona, na ga an karya manaja daya, amma wasu abokan aikina sun ce wadanda aka karya sun fi mutum daya”, in ji majiyar.
Wannan rikici dai na zuwa ne a daidai lokacin da direbobin motocin kamfanin na Dangote ke zargin akwai wasu daga cikin manajojin da ke yi musu kwange a wajen biyansu hakkokinsu, lamarin da ya yi sanadiyyar suka tsunduma yajin aiki na sai baba ta gani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jam’iyyar EFF ta Afirka ta Kudu ta yi tir da amincewar Nijeriya kan harin Amurka

Jam’iyyar Afirka ta Kudu ta dan gwagwarmayar adawa da Turawa Julius Malema (EFF) ta yi Allawadai da yadda Nijeriya ta amince da harin Amurka a...

Mun nemi taimakon Turkiyya wajen yakar matsalar tsaro a Nijeriya – Shugaba Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta nemi taimakon kasar Turkiyya wajen yakar matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Nijeriya.   Tinubu ya bayyana...

Mafi Shahara