DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya na ba kasashen Togo da Benin wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24, in ji kamfanin TCN

-

Manajan Daraktan 
kamfanin rarraba wutar lantarki a Nijeriya Sule Abdul’aziz ya sanar cewa kasar na ba kasashe makwabta na Togo da Benin wutar lantarki ta sa’o’i 24 a duk rana.
Sule Abdul’aziz ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi a wani shirin gidan talabijin na Channels.
 Ya kara cewa Nijeriya na samar da lantarkin ga wadannan kasashe kuma suna biya yadda ya kamata. 
Sai dai ya ce ko a Nijeriya ma akwai masu samun wutar lantarki ta sa’o’i 24, musamman waɗanda ke saman tsarin Band A, suna samun ta sa’o’i 20-22, kama yadda jaridar Punch ta rawaito.
Kamfanin TCN dai ya ce an tsara ba waɗanda suke saman tsarin Band A, wutar lantarki ta sa’o’i 20-24, sai na saman Band B aka tsara ba su wutar lantarki ta sa’o’i 16-20, sai waɗanda ke saman tsarin Band C aka tsara ba su wutar lantarki ta sa’o’i 16-20 a rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara