DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Atiku da Wike sun hadu, karon farko tun bayan zaben 2023, sai dai babu tabbacin ko sun gaisa

-

A karon farko tun bayan zaben 2023, Atiku Abubakar da Nyesom Wike sun hadu wajen guda don taron jam’iyyar PDP.

Sai dai Premium Times ta ce babu tabbacin ko sun gaisa a wajen taron.
Atiku Abubakar dai shi ne tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, yayin da Nyesom Wike ya yi Gwamnan jihar Rivers sau biyu, yanzu kuma shi ne ministan Abuja a gwamnatin APC.
Sauran wadanda suka halarci taron akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Abba Moro da Sanata Aminu Waziri Tambuwal, akwai tsohon Gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP Ahmad Makarfi, da tsohon Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu, tsohon Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da tsohon Gwamnan jihar Plateau Jonah Jang.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe daga ranar 18 ga Agusta a Nijeriya

Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta sanar da ranar 18 ga watan Agusta, 2025 a matsayin ranar da za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe a...

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Mafi Shahara