DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An sake zaben Abdel-fatah Al-sisi a matsayin shugaban kasar Egypt karo na uku

-

Hukumar zaben kasar Masar ta sanar cewa shugaba Abdel-fatah Al-sisi ya sake yin nasara karo na uku bayan zaben da aka gudanar makon jiya.
Al-sisi ya zamo shugaban kasar Masar a shekarar 2014, aka sake zabensa a shekarar 2018, sai yanzu da zai ci gaba da jagorantar kasar har zuwa 2029 da kundin mulkin kasar ya ce nan ne magaryar tukewa.
Hukumar zaben dai ta ce Abdel-fatah Al-sisi ya lashe zaben ne da kaso 90% na yawan kuri’un da aka kada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dokokin Amurka na neman haramta biza da toshe dukiyar mambobin Miyetti Allah

Sabon kudiri da majalisar dokokin Amurka ke tattaunawa ya bukaci kakaba takunkumin biza da kulle dukiyar mambobin kungiyoyin Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria...

Baba-Ahmed ya bukaci Tinubu ya fito ya yi ma ‘yan Nijeriya bayani kan barazanar Amurka

Tsohon mai ba wa shugaban kasa shawara, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaba Bola Tinubu da ya fito fili ya yi wa ’yan Nijeriya jawabi...

Mafi Shahara