![]() |
| Donald Trump |
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, za a saka harajin kashi 14 cikin 100 na kayan da ake fitarwa daga Nijeriya zuwa Amurka.
Matakin, wanda aka bayyana a yayin wani taron ”Make America Wealthy Again” a ranar Laraba, wani bangare ne na dabaru da nufin daidaita kasuwancin duniya da kuma magance shigar da kayayyakin da basu dace ba.
Sabon harajin kashi 14 cikin 100 da aka gabatar ya nuna wani gagarumin sauyi a huldar kasuwanci tsakanin Amurka da Nijeriya, inda gwamnatin Amurka ta yi nuni da cewa ana fuskantar rashin daidaiton ciniki a tsakani.
A cewar gwamnatin Trump, Nijeriya na sanya harajin kashi 27 cikin 100 kan kayayyakin da Amurka ke fitarwa zuwa kasar, wanda hakan kusan ninki biyu ne na abinda Amurka zata karba a matsayin haraji daga kayayyakin da suka shiga kasar daga Najeriya.




