DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Najeriya ta kwaso yan kasar Kusan 200 da aka kulle a gidan yarin Libya

-

Gwamnatin Najeriya
ta kwaso yan asalin kasar 161 da aka daure su a gidajen yarin kasar Libya daban-daban
sakamakon aikata laifukan da suka sabawa ka’idar yin kaura.

Jakadan Najeriya a Libya Ambasada Kabiru Musa ne ya bayyana hakan a wata
sanarwa da ya fitar ga manema labarai a birnin tarayyar kasar Abuja.

A cewar Ambasada Musa gwamnatin Najeriya
ta rika kai gwauro da kai mari wajen ganin an saki mutanen da aka garkame a
gidan yarin don basu damar komawa gida, da nufin sake gina rayuwar su.

Sanarwar ta kuma kara da cewa tuni
mutanen suka isa Najeriyar, yayin da aka gargade su da su kaucewa yunkurin tsallakawa
zuwa turai ta barauniyar hanya don gudun fadawa hannun hukumomi ko kuma bata
gari.

Wannan dai ba shine karon farko da ake samun ‘yan Najeriya da dama na
tsallakawa zuwa turai da saharar Libya ba, inda kuma a mafi yawan lokuta suke
gamuwa da masu garkuwa da mutane ko yan fashi ko kuma  a wasu lokutan su ci karo da jami’an tsaro.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan sanda a jihar Nasarawa sun kama wata mata da makamai za ta kai su Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa jami’anta, sun kama wata mata da ake zargi da safarar makamai ga barayin daji. Mai magana da...

Kudurin dokar tilasta yin zabe ga kowane dan Nijeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai

By Salim Muhammad Musa Kudurin na gyaran dokar zabe ta shekara ta 2022, ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai a wannan Alhamis. Idan har wani...

Mafi Shahara