Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAn ji karar harbe-harbe a wurin taron magoya bayan Wike a jihar...

An ji karar harbe-harbe a wurin taron magoya bayan Wike a jihar Bayelsa

An shiga cikin tashin hankali a birnin Yenagoa ta jihar Bayelsa, bisa karar harbe-harbe da aka ji a wurin masu biyayya ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike karkashin wata kungiya mai suna NEW Associates.

Kungiyar ta shirya taron ne karkashin jagorancin George Turnah, jigo a jam’iyyar PDP a jihar.

Ana ci gaba da gudanar da taron ne a lokacin da aka yi ta jin karar harbe-harbe a yankin, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan harbe-harbe, sakataren kungiyar NEW Associates a jihar Bayelsa, Comrade Ebilade Ekerefe, ya ce za su ci gaba da gudanar da taron.

A halin yanzu, magoya bayan NEW Associates sun sake haduwa don ci gaba da gangamin taron.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata