DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedKarancin abinci mai gina jiki da ciwon suga ne ke kara ta'azzara...

Karancin abinci mai gina jiki da ciwon suga ne ke kara ta’azzara tarin fuka a Nijeriya – Ministan lafiya

Farfesa Muhammad Pate 

Ministan lafiya Farfesa Muhammad Pate, ya ce rashin samun wadataccen abinci mai gina jiki da cuta mai karya garkuwar jiki da ciwon suga da shan sigari da kuma shan giya a tsakanin yan shekaru 15 zuwa 44 ne abinda ya fi ta’azzara kamuwa da cutar tarin fuka a Nijeriya.

Farfesa Pate ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a wani bangare na bikin ranar tarin fuka ta duniya, inda yace, Nijeriya tana cikin kasashe goma da suka fi fama da nau’ukan tarin fuka, da kuma masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki, yana mai cewa kimanin ‘yan kasar dubu 71 ne suka kamu da cutar tarin fuka a shekarar 2023.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewa mutum daya ne cikin yan Nijeriya hudu ke da cikakken sani game da illar cutar tarin fuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata