DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta bukaci sabon shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali...

Gwamnatin Nijeriya ta bukaci sabon shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali ya mayar da hankali wajen sauya tunanin daurarru

Gwamnatin tarayya ta bukaci sabon shugaban hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali na kasar Sylvester Nwakuchi, da ya mayar da hankali wajen sauya tunani da kuma rayuwar daurarru maimakon hukunta su kawai.

Ministan harkokin cikin gida Dr. Olubunmi Tunji Ojo ne ya yi wannan kira yayin bikin nadin da aka yi wa sabon shugaban hukumar a birnin Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A jawabinsa, ministan ya jaddada muhimmancin shugabanci na gari ta hanyar rikon gaskiya da amana wajen kawo sauyi mai inganci a tsarin gidajen ajiya da gyaran hali, tare da dora wa sabon shugaban alhakin tabbatar da sauyi cikin watanni 19 masu zuwa.

A nasa bangaren, Sylvester Nwakuchi ya yi godiya da sabon mukamin naa tare da bayyana shirin sa na inganta tsaro, rage cinkoso, samar da gine gine da kuma walwalar ma’aikata.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata