Sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume, ya nesanta kansa da mai taimaka masa Andrew Torhile Uchi, wanda a yanzu haka hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ke bincikensa.
Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin Segun Imohiosen, ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar jiya Lahadi a Abuja.
Hukumar EFCC dai zargin Uchi da cin hanci da rashawa da kuma safarar kudade sama da biliyan 10.