DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar dokokin jihar Rivers ta tafi hutu bayan Gwamna ya sake rubuta mata bukatar gabatar da kasafin kudi

-

Sim Fubara

Sa’o’i kadan bayan gwamnan jihar Rivers Similanayi Fubara ya sake mika wata bukata ga majalisar dokokin jihar ta gabatar da kudirin kasafin kudi na shekarar 2025, majalisar ta dage zaman ta har sai baba ta gani.

Dage zaman majalisar ya zo ne sa’o’i kadan bayan da gwamnan ya ce ya aika wa majalisar wasika karo na biyu domin gabatar da kasafin kudin jihar na 2025.

An cimma matsayar dage zaman har sai baba ta gani a zauren majalisar karkashin jagorancin kakakin majalisar Martins Amaewhule.

Gwamna Fubara a cikin wasikar da ya aike wa shugaban majalisar ya sanar da majalisar aniyarsa ta gabatar da kasafin kudin a ranar 19 ga Maris, 2025.

A cikin wasikar, ya bukaci majalisar ta kuma zabi duk ranar da ta dace banda ranar 19 ga Maris domin gabatar da kasafin kudin.

Bayan ya kasa cika wa’adin sa’o’i 48 da ‘yan majalisar suka ba shi, Fubara ya je harabar majalisar a ranar Laraba domin gabatar da kasafin kudin, amma an kulle kofar.  

Dage zaman majalisar yazo ne a daidai lokacinda gwamnan ke kokarin sasantawa da ‘yan majalisa 27 da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, wanda ya gaje shi, bayan hukuncin kotun koli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Atiku Abubakar ya caccaki hukumar EFCC kan tsare tsohon dan majalisa Gudaji Kazaure

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, kan tsare tsohon dan...

Gwamnatocin Pakistan da Indiya sun amince da tsagaita wuta a Asabar dinnan

Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya sanar a shafinsa na X cewa, kasashen sun amince da Shirin tsagaita wuta cikin gaggawa. Shugaba Trump ya sanar...

Mafi Shahara