Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnonin PDP sun kira taron kan sauyin sheka da jiga-jigan jam'iyyar ke...

Gwamnonin PDP sun kira taron kan sauyin sheka da jiga-jigan jam’iyyar ke yi

Gwamnonin jam’iyyar PDP za su yi taro a Abuja akan sauyin shekar da ‘yan jam’iyyar ke yi a kwanakinnan.

Wannan ya biyo bayan ficewar gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori da Dr. Ifeanyi Okowa, da sauran ‘yan jam’iyyar PDP a jihar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnonin sun gana makonni uku da suka gabata a Ibadan inda suka bayyana cewa jam’iyyar ba za su shiga tattaunawar hadaka da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ke jagoranta ba.

Gwamnonin za su yi taron ne a gidan gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad da ke Asokoro a Abuja da nufin shawo kan matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata