Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da sauki, inda ya nuna faduwar farashin shinkafa da kayan masarufi a matsayin shaida.
Yayin bikin cikar gwamnatinsa shekaru biyu, Tinubu ya ce duk da tsadar rayuwa, ana samun saukin hauhawar Farashin kayan masarufi.
A watan Maris din 2025, binciken kamfanin dillacin labarai na Nijeriya NAN ya tabbatar da saukar farashin shinkafa a kasuwanni da dama a fadin Najeriya.



