Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta ja kunnen 'Sarkin Mota' kan tsokanar ma'aikatan gwamnati a...

Gwamnatin Nijeriya ta ja kunnen ‘Sarkin Mota’ kan tsokanar ma’aikatan gwamnati a bidiyonsa

Gwamnatin tarayya ta gargadi dillalin motoci a Abuja, wanda aka fi sani da Alamin Sarkin Mota, kan yi wa ma’aikatan gwamnati ba’a a cikin bidiyon talla da yake yi.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA ce ta yi wannan gargadi a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun babban daraktanta, Lanre Issa-Onilu, a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sarkin mota ya yi kaurin suna wajen bayyana cewa motocin da yake talla sun fi karfin ma’aikaci ya siya, saboda tsadarsu.

A saboda haka hukumar ta gargadi dillalin motocin da ya kiyaye irin kalaman da yake yi a duk lokacin da yake kokarin tallata motocinsa domin kaucewa cutar da jajirtattun ma’aikatan Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata