Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tana sane da wani labari da ta kira na karya da ake yadawa musamman a kafar sadarwar X cewa barayin daji sun karbe ikon yankin karamar hukumar Kankara ta jihar.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar DSP Sadiq Abubakar Aliyu ya fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce kwata-kwata babu kanshin gaskiya a labarin, an kirkiro shi ne kawai don a jefa tsoro a zukatan jama’a musamman na yankin karamar hukumar Kankara da sauran ‘yan jihar Katsina.
Rundunar ‘yan sandan ta bukaci mutane da su yi watsi da wadannan bayanai da ta kira na karya da ke yawo l. Sannan ta ba da tabbacin cewa tana nan tana bincike don zakulo waÉ—anda suka kitsa labarin don daukar matakin da ya dace a kansu.



