DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An kori wasu jami’an ‘yan sanda uku bisa zargin rashawa da garkuwa da mutane

-

 

Police

Google search engine

Rundunar ‘yan sandan jihar Abia da ke kudu maso gabashin Nijeriya ta kori wasu jami’anta uku bisa zarginsu da rashin da’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Maureen Chinaka ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Chinaka, ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Abia, Danladi Isa ne ya  bada umarnin korar jami’an ‘yan sandan.

Kakakin ‘yan sandan ta bayyana sunayen jami’an da aka kora da suka hada da Jonas Nnamdi,  sai James Daniel, da Ifeanyi Emeka.

A cewar ta an kori jami’an uku ne saboda dabi’u mara sa kyau da suka hada da rashawa, hada baki, da satar  mutane ta hanyar yin garkuwa dasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnan Kebbi ya soki rundunar sojin Nijeriya kan yadda take yakar rashin tsaro

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya nuna rashin gamsuwa da tsarin da rundunar soji ke amfani da shi wajen yakar rashin tsaro yana mai kira...

Sace dalibai na barazana ga makomarsu a Arewacin Nijeriya – Amnesty International

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International a Nigeria ta yi gargadin cewa yawaitar sace dalibai a makarantun arewa na iya karya ilimi, tare...

Mafi Shahara