DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba a hango Atiku Abubakar ba a taron jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso Gabas da ya gudana a Bauchi ba

-

Babbar jam’iyyar adawa ta Nijeriya PDP a yankin Arewa masu gabas ta gudanar ta taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ya gudana a jihar Bauchi.

Google search engine

Taron dai ya samu halartar dukkanin gwamnonin ta uku da suka hada da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da na jihar Taraba Dr Agbu Kefas da kuma Ahmad Umar Fintiri na jihar Adamawa.

Haka kuma taron ya samu halartar Sanatoci da ‘yan majalissun wakilai da kuma ‘yan majalisar jiha daga shiyyar.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa tsohun shugaban kasar Atiku Abubakar bai samu halartar taron ba ko aike wa da wakili a wajen taron.

Wannan dai a iya cewa ko bai rasa nasaba da rikicin cikin gida da jam’iyyar ta PDP ke fama da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babban layin wutar lantarkin Nijeriya National Grid ya fadi

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya fadi Litinin din nan, lamarin da ya jefa ’yan Nijeriya da dama cikin duhu bayan da manyan tashoshin...

‘Yan bindiga sun kai hari a wani kauye na jihar Kebbi

’Yan bindiga sun kai hari a kauyen Gebbe da ke karamar hukumar Shanga a jihar Kebbi, inda rahotanni ke nuna an rasa rayuka yayin da...

Mafi Shahara