DCL Hausa Radio
Kaitsaye

A hukumance, ECOWAS ta amince da fitar kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar

-

Kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, ta umurci mambobinta da su ci gaba da mu’amala da kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar.
Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta amince da fitar kasashen uku da ga cikin ECOWAS a hukumance da yau Laraba 29 ga watan Janairun 2025.
Wata sanarwar da kungiyar ta fitar a Laraba, ta ce ficewar kasashen ba zai hana ci gaba da mu’amala tsakanin al’ummar kasashen ba ciki har da harkokin kasuwanci da shige da fice.
Tuni dai kasashen na Burkina Faso, Nijar da Mali suka kafa sabuwar kungiyar kawance da suka kira Alliance des États du Sahel (AES) (AES) a madadin ECOWAS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Atiku martani cewa babu yunwa a Niijeriya

Fadar shugaban kasa ta ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tafiya kan madaidaiciyar hanya, tana mai musanta ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da...

Kotu ta daure wani dan Nijeriya a Amurka kan laifin zambar kudin gado

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Ehis Lawrence Akhimie hukuncin daurin shekaru fiye da takwas bayan an same shi...

Mafi Shahara