DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni a kowane mataki na gwamnati da su rika tabbatar da gaskiya da rikon amana ga wadanda suke shugabanta

-

 

Muhammad Buhari

Google search engine

Buhari ya bayyana haka ne a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar gwamnatin jihar Katsina, a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC gabanin zaben kananan hukumomin jihar a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Tsohon shugaban kasar ya ce wadannan abubuwa na da matukar mahimmanci wajen samun daidaito a tsakanin al’umma da shugabanni da ke jagorantar su a dukkan matakai.

A nasa bangaren, Gwamna Dikko Radda, ya ce jihar ta kuduri aniyar gudanar da zabe na gaskiya, sai dai gwamnan ya umurci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar da su hada kai don tabbatar da nasarar jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara