DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeKetareSojojin kasar Gabon sun sanya ranar zaben shugaban kasa bayan juyin mulkin...

Sojojin kasar Gabon sun sanya ranar zaben shugaban kasa bayan juyin mulkin 2023

 

Sojojin kasar Gabon sun sanya ranar zaben shugaban kasa, bayan hambarar da gwamnatin farar hula da Ali Bongo

Za a dai gudanar da zaben ne a ranar 12 ga watan Afrilun, 2025, wanda shugaban rikon kwarya bayan juyin mulkin Janar Brice Oligui Nguema, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara.

A watan Agustan 2023 ne dai sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Ali Bongo da ya yi shekaru 14 yana shugabancin kasar, bayan da shi kuma ya karbi tafiyar da ragamar kasar bayan mahaifinsa Omar Bongo ya rasu wanda ya yi shekaru 41 yana mulkin kasar ta Gabon.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata