DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedHadakar kungiyoyin Arewacin Nijeriya CNG ta yi Allah wadai da amincewar da...

Hadakar kungiyoyin Arewacin Nijeriya CNG ta yi Allah wadai da amincewar da Hukumar sadarwa ta kasar NCC ta yi wa kamfanonin sadarwa na karin kashi 50% na kudin kira da na data a kasar

 

CNG

A wani bayani da Kodinetan kungiyar na kasa Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi ya fitar, yace wannan matakin zai ƙara jefa al’umma cikin halin matsin rayuwa da suke ciki.

Kungiyar ta nanata cewa kalaman gwamnati na tuntubar masu ruwa da tsaki shaci-faɗi ne domin ‘yan Nijeriya dake shan wahalar saka kudin sadarwa ba su cikin wannan tuntubar.

Da wannan ƙarin da aka yi, kudin kira za su tashi daga  N11 zuwa N16.50 duk minti ɗaya, inda tura sako zai kai N6 daga Naira 4, hakama kudin data zai tashi daga N350 zuwa N431.25 akan kowace 1gb.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata