DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mutane 86 suka mutu sanadiyar fashewar motar man fetur jihar Neja, an binne 80 a kabari daya – Hukumar NSEMA

-

Biyo bayan fashewar motar man fetur a mararrabar Dikko Junction, dake karamar hukumar Gurara jihar Niger, hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar NSEMA ta ce zuwa yanzu mutum 86 suka mutu.
Wani bayani da daraktan yada labarai na hukumar Abdullahi Baba-Arah ya fitar, ya ce hukumar ta tattara gawarwakin mutanen ne tare da taimakon jami’an karamar hukumar Gurara da kuma jami’an sa kai.
Daga cikin wadanda suka mutu an binne mutum 80 a kabari daya a cibiyar kafiya ta Dikko yayinda biyar aka hannunta su ga ‘yan uwansu, mutum daya kuma ya mutu daga baya saboda raunin da ya ji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun halaka jigo a jam’iyyar APCn jihar Zamfara

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun halaka wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Umar Moriki da safiyar ranar Asabar. Gidan talabijin...

Jam’iyyar PDP ta kori su Wike daga cikinta

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Nijeriya ta bayyana korar ministan birnin Abuja Nyesom Wike da wasu 'ya'yanta daga cikinta. Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin kudancin...

Mafi Shahara