DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya yi jinjina ga Gwamnonin Nijeriya da suka goyi bayan kudirin garambawul ga dokar haraji

-

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yabawa gwamnonin jihohin kasar bayan da suka amince da kudirin garambawul na dokar haraji, dake gaban Majalisu.

Shugaban ya kuma ya yabawa shugaban kungiyar gwamnonin gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq bisa hade kan gwamnonin da yayi suka aminta da lamarin na haraji.
Ta cikin sanarwar da jami’in yada labaran sa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce gyara fare da yin kwaskwarima ga tsohon tsarin karbar haraji na da matukar muhimmanci.
A karshe ya bukaci Majalisar dokoki da su yi hanzarin sahale kudirin domin ya zama doka da al’ummar Najeriya za su amfana da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara