Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedBa da gan-gan harin da muke kai wa 'yan ta'adda ke shafuwar...

Ba da gan-gan harin da muke kai wa ‘yan ta’adda ke shafuwar fararen hula ba – Sojojin Nijeriya

 Ba da gan-gan harin da muke kai wa ‘yan ta’adda ke shafuwar fararen hula ba – Sojojin Nijeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce duk hare-hare ta sama da take kai wa ga masu aikata laifukan ne ba fararen hula ba.

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka a wata hira da yayi a gidan Talabiji na Arise TV, a lokacin da yake mayar da martani game da mutuwar fararen hula sama da 10 sanadiyar harin da sojojin suka kai kwanan nan a Zamfara.

Janar Christopher Musa, wanda ya bayyana cewa sojoji sun bi ka’idoji masu tsauri kafin aiwatar da duk wani hari ta sama, ya jaddada cewa sojojin na kai hare-hare ta sama daidai gwargwado domin kawar da yan ta’adda dake addabar wasu sassan jihohin Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata