DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan jihar Zamfara Dauda ya ba ma’aikatan jihar ‘bonus’ don saukaka musu rayuwa

-

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da ba ma’aikatan gwamnati a jihar kaso 30% na albashinsu a matsayin wani ‘hasahi’ da zai rage musu radadin rayuwa.
A wata sanarwa daga shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Ahmad Aliyu Liman, ta ce karimcin bai tsaya ga ma’aikatan gwamnati kadai ba, hada ‘yan fansho da suka yi ritaya daga aiki.
Sanarwar ta ce wannan karimcin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na inganta rayuwar ma’aikata da sauran daukacin al’ummar jihar.
Gwamna Dauda Lawan ya bukaci ma’aikatan jihar da su mayar da biki ta hanyar jajircewa wajen aiki don gina jihar ta zarta tsara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050,...

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba...

Mafi Shahara